News
IPMAN ta musanta kara farashin Man Fetur zuwa 700
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta musanta zargin da ake yiwa kungiyar na kara farashin man zuwa naira 700.
Shugaban kungiyar na Kudu maso Yamma Dele Tajudden ne ya musanta karin kudin man fetur din a zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Indaranka:An Sa Albashin Naira Miliyan 104 Ga Mai Son Aikin Kula Da Kare
Shugaban kungiyar dillalan man fetur din ya bukaci al’umma dasu yi watsi da jita jitar da ake yadawa kan karin kudin man. Ya ce farashin man fetur ba zai wuce yadda ake saida shi a yanzu ba.
Advertisements
