News
Gwamnati Ta Bayyana Yankunan Da Za A Iya Samun Ambaliyar Ruwa A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwar hasashen ambaliya a shekara ta 2023, inda ta ce jihohi 14 da al’ummomi 31 za su iya ganin ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da muhalli ta tarayya ta fitar.
Gwamna Abba Na Jihar Kano Ya Dora Kwamishinoninsa A Matakin Gwaji Na Wata 6
A cewar sanarwar, an gano jihohin da al’ummomin da suka hada da:
Kano inda ake da ran za a samu ambaliya a kananan hukumomi Sumaila da Tudun Wada
Sai jihar Plateau da jihar Sokoto.
Sai kuma jihohin Delta, Kaduna, Akwa Ibom, Adamawa, Katsina da Kebbi.
Sai Zamfara, Borno, Jigawa, Kwara da jihar Niger.
Gwamnatin ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin kiyaye asarar rayuka da dukiyoyi.
