News
Dole Mu Kalubalanci Duk Wani Yunkuri Na Kuntatawa ‘Yan Najeriya – NLC,
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi barazanar daukar mataki a hannunta biyo bayan karin farashin man fetur.
Kungiyar ta NLC a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugabanta na kasa Joe Ajaero, ta zargi gwamnatin Tinubu da tatse talakawa domin hidimtawa masu hannu da shuni da kuma jefa ‘yan Najeriya cikin wahala.
Tinubu Ya Bada Umarnin Sake Nazari Kan Tallafin Naira Dubu 8 Ga Gidajen Talakawa Masu Rauni
Ya kuma yi nuni da kudirin biyan ‘yan majalisar dokokin kasarnan zunzurutun kudi har naira biliyan 70 da Naira billiyan 36 ga bangaren Shari’a yana maibayyana hakan amatsayin mafi girman karkatar da kudade cikin aljihun jami’an gwamnati.
Ita kuwa, kungiyar kwadago ta TUC ta bakin mataimakin shugabanta na kasa, Tommy Etim, ita ma ta caccaki gwamnatin tarayya kan karin farashin man fetur, inda ta ce yanzu kasarnan na fuskantar rudanin tattalin arziki.
-
News15 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
