News
Tinubu Ya Bada Umarnin Sake Nazari Kan Tallafin Naira Dubu 8 Ga Gidajen Talakawa Masu Rauni
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a sake fasalta shirin bada kudi Naira dubu 8 da aka tsara domin tallafi ga gidajen Talakawa da sukafi rauni a Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce umarnin ya biyo bayan sauraron ra’ayoyin da ‘yan Najeriya suka bayyana akan tsarin.
Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Daukar Hayar Kungiya Domin Bata Sunan Tsohuwar Gwamnati
Alake ya ce shugaban kasar ya kuma bayar da umarnin a gabatarwa ‘yan Najeriya gaba daya tsarin tallafin da gwamnati zata bayar domin ba iya shirin tallafin kudi ba ne kadai a jimillah tsare-tsaren Rage radadin.
Alake ya ce shugaba Tinubu amatsayin jagora mai sauraron Jama’arsa ya kuma ba da umarnin a gaggauta sakin takin zamani da hatsi ga manoma da gidaje miliyan 50 a fadin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
