Connect with us

News

Rundunar Sojin Ruwa Sun Dakile Yunkurin Balle Rumbun Ajiyar Abinci A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Rundunar sojin ruwa ta kasa tace tayi nasarar dakile yunkuri fasa rumbunan ajiyar kayan abinci ajihar Kano a ranar da kungiyoyin kwadago suka gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar Rayuwa.

Shugaban kwalejin horas da jami’an sojojin ruwa dake Dawakin Tofa, Usman M Bugaji ne ya bayana hakan yayin faretin bankwana bayan ya shafe kusan shekara biyu a matsayin kwamandan kwalejin.

Kasar Senegal tace a shirye take ta dauki matakin soja kan Jamhuriyar Nijar

Bugaji yace an samu nasarar hana wasu matasa balle rumbun ajiyar abinci dake kasuwar Dawanau a cikin dare yayin zanga-zangar kungiyoyin kwadago.

Haka kuma yace rundunar tayi nasarar dakile wani yunkurin yin safarar wasu mata guda 18 daga jahar Kano zuwa kasar Libya.

Arewa radio ta rawaito cewa sabon kwamandan kwalejin Comodore James Kolade Adedeji, ya ce zai cigaba da bunkasa alakar dake tsakanin kwalejin da kuma al’ummar yankin domin samar da ingantaccen tsaro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending