News
Nasir El-Rufai na cikin mutum uku da ba a tabbatar wa mukaman minista ba
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai na cikin mutum uku da Majalisar Dattawan Nijeriya ba ta tabbatar wa mukaman minista ba.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman da ta yi ranar Litinin a yayin da suka tabbatar wa mutum 45 da mukaman minista.
Hukumar NSCDC ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin barayin shanu ne a jihar Jigawa.
Sauran mutanen da ba a tabbatar wa mukaman ba su ne tsohon gwamnan riko na jihar Taraba Sani Danladi da kuma Stella Okotete.
An nada El-Rufai, Badaru da Wike a matsayin ministocin Tinubu
Majalisar dattawan ta bukaci a kara binciken sirri a kansu.
Da ma dai a lokacin da ya je gaban majalisar domin a tantance shi, Nasir El-Rufai ya fuskanci tambayoyi daga wurin wani dan majalisar dattawa da ya ce an aika masa wasikar korafi a kan tsohon gwamnan na jihar Kaduna game da kalamansa kan tsaro da hadin kan Nijeriya.
