News
Hukumar ICPC Ta Fara Bincike Kan Zargin cin Hanci da Rashawa Da ake Yiwa Tsohon Ministan Shari’a
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC a hukumance ta tabbatar da fara Gudanar da bincike a hukumance kan zargin cin hanci da rashawa da ya shafi Tsohon Babban lauyan Gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami kuma Surukin Tsohon Shugaban Kasa Buhari.
Anyi cikakken bayanin wannan bincike ne, A cikin wata sanarwa mai kwanan watan Yuli 19, 2023, Wanda H.S. Folaranmi Ya Fitar.
A yayin da take mayar da Martani kan koken da cibiyar albarkatun ƙasa ta Human and Environmental Development Agenda (HEDA), Wata ƙungiya mai zaman kanta ta Najeriya ta shigar Gaban, ICPC ta bayyana kudurinta na magance matsalolin da aka taso. Shugaban ƙungiyar, Olanrewaju Suraju, ne Ya miƙa buƙatar A Ranar 10 Ga Watan Yuli, 2023.
Takardar koken ta kawo misalai daban-daban na Rashin da’a da Kuma rashin bin ka’ida da suka shafi Abubakar Malami a lokacin da yake riƙe da muƙamin Babban lauya Kuma Ministan shari’a. Waɗannan zarge-zarge sun kunshi batutuwa da dama, Da suka haɗa da rabon kyaututtukan Motoci, Gwanjon jiragen Ruwa da aka kama, da katsalandan a bincike, Da kuma zargin hannu a ayyukan damfara.
HEDA ta Bayyana damuwar ta Sannan ta Buƙaci a Gudanar da cikakken bincike kan waɗannan munanan zarge-zarge don tabbatar da bin doka da oda da kuma Tabbatar da bin diddigin masu riƙe da muƙamin Gwamnati.
Matakin da ICPC ta ɗauka na fara Gudanar da bincike ya nuna irin yadda ta dage wajen Tabbatar da Gaskiya, Da kuma adalci a cikin sassan Gwamnatin Najeriya. Wannan matakin na nuna muhimmancin Tabbatar da cewa anyi nazari sosai kan zarge-zargen cin hanci da Rashawa da kuma cin zarafi na ofis da kuma magance sahihancin cibiyoyin Gwamnati.
