News
Cikin Kwana 100 Rundunar ‘Yan Sanda A Jihar Kano Ta Kama Mutane Sama Da Dubu 1 Bisa Zargin Aikata Laifuka
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, yace an kama mutane sama da dubu 1 da ake zargi da aika laifuka, tare da gurfanar da su a gaban kotu a cikin kwanaki 100 da ya yi da kama aiki.
Gumel ya bayyana haka ne a shalkwatar ‘yan jarida ta jihar Kano a lokacin da yake bayyana nasarorin da ya samu a cikin kwanaki 100 da suka gabata, yayin wani taron manema labarai na musamman, wanda shugabannin kungiyar ‘yan jaridu reshen kafafen yada labarai suka shirya.
Kungiyar KwadagoTa NLC Ta Gargadin Gwamnati Kan Duk Wani Yunkuri Na Karuwar Farashin Litar Man Fetur
A cikin kwanaki 100 da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano ya fara aiki an kama sama da mutane dub 1, an binciki wadanda ake zargin tare da wasu adadi mai yawa daga cikinsu wadan har yanzu ke gidan yari suna jiran shari’a bisa laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, kisan kai da ‘yan daba da masu rike muggan makamai da masu fataucin muggan kwayoyi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce cikin mutanen akwai ‘yan fashi da makami 117, masu garkuwa da mutane 25, barayin shanu 6, masu safarar mutane 17, wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi 34, barayin motoci 18, barayin motoci su 27, barayin baburin adaidaitasahu 16, barayin babur mai kafa 2 s 58 sai 19 da ake zargi da damfara da 636 da ake zargin ’yan daba ne.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
