Connect with us

News

Kungiyar KwadagoTa NLC Ta Gargadin Gwamnati Kan Duk Wani Yunkuri Na Karuwar Farashin Litar Man Fetur

Published

on

Kungiyar kwadogo ta NLC ba zanga zanga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta sake gargadin cewa mambobinta za su fara yajin aikin a fadin kasarnan ba tare da wata sanarwa ba idan ‘yan kasuwar suka kara farashin man fetur ba tare da kammala tattaunawar da ake yi ba.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, yayin da yake tabbatar da hakan a ranar Litinin, ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta dakatar da matsalar faduwar darajar Naira.

Advertisement

Juyin mulkin Nijar: Dattawan Katsina sun gargadi ECOWAS game da tsoma baki  Akan Jamhuriyar Nijar.

Da yake jawabi a taron kungiyar kwadago ta Afirka da ke gudana a Abuja, Ajaero ya shawarci gwamnatin tarayya da ta canza munanan manufofin tattalin arziki da ke sanya albashin ma’aikata na tashi ba’a bakin komai ba.

Barazanar da kungiyoyin kwadagon suka yi ta biyo bayan rade-radin da akeyi cewa ‘yan kasuwar man fetur, na iya kra kudin litar mai zuwa 720 a makonni masu zuwa idan dala ta ci gaba da tashi zuwa 950.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending