Connect with us

News

Matan Aure Sunyi Zanga-Zanga Kan Yunwa Da Tsadar Abinci A Kaduna

Published

on

Mata na zanga zanga a kaduna

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Wasu matan aure a karamar hukumar Igabi sun yi zanga-zangar lumana don nuna damuwa kan halin da ake ciki Matan su ka ce sun fito ne don rokon Shugaba Tinubu ya yi wani abu don kawo karshen tsadar abinci da yunwa Wata dattijuwa mai shekaru 60 ta tabbatar da cewa akwai yara biyu da su ka mutu saboda tsabar yunwa a garin.

Matan aure daga garin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna damuwarsu da halin da ake ciki.

Advertisement

Za Mu Cafke duk Wasu kwararrababbun Motoci Tare da Masu su – FRSC

Matan auren da suka hada da yaransu sun yi wannan tattaki ne musamman don nuna damuwa da irin yunwa da ake ciki da tsadar kayayyaki.
An Gudanar Da Zanga-Zangar Ne Don Nuna Damuwa Da Halin Da Ake Ciki.

Wasu daga cikinsu sun roki Shugaba Bola Tinubu da ya kawo musu dauki inda su ka ce ba su taba shiga irin wannan hali ba.

Advertisement

Wata dattijuwa duk da rashin lafiyarta ta samu shiga cikin masu zanga-zangar da ‘ya’yanta marayu guda biyar da ta ce su na matukar bukatar abinci mai gina jiki.

Meye ma su zanga-zangar a Kaduna ke bukata?

Advertisement

Ta bayyana cewa rasuwar kanin mijinta wanda ya dadeya na taimaka musu bayan rasuwar mijinta shi ya jefata cikin wannan hali inda ta ce babu yadda ta iya dole rokon jama’a ta ke don samun abin tabawa.
Wata dattijuwa mai shekaru 60 ta bayyana cewa yara biyu a garin sun mutu saboda tsananin yunwa inda ta alkanta hakan da rashin iya kawo abinci daga iyayensu, cewar Leadership.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ba wai taimakonsu su ke son a yi ba, amma su na rokon Shugaba Tinubu da ya kawo karshen tsadar abinci saboda su sa mu su siya a farashi mai rahusa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending