News
Nyesom Wike ya yi barazanar rusa gidaje a ranarsa ta farko a ofishi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Sabon ministan babban birnin tarayyar Abuja, Nyesom Wike, ya yi barazanar fara rusa gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba.
Wike ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi domin soma aiki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta rufe gidajen mai guda biyar
“Idan kun gina gidajenku a wuraren da aka saba ka’ida, sai an rusa su,” in ji Wike.
Tsohon gwamnan Ribas din yana cikin ministoci 45 da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da su a fadarsa da ke Abuja.
Wike ya sha alwashin yin tir da tsarin da ke kawo cikas ga taswirar babban birnin tarayyar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
