News
Tinubu zai gana da Joe Biden a Amurka
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka Joe Biden a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a watan gobe, a cewar mai magana da yawunsa.
Za a gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ne daga ranar 18 zuwa 26 ga watan Satumba a birnin New York.
Gwamnatin Sojin Jamhuriyyar Nijar Ta Musanta Korar Jakadan Najeriya
Wata sanarwa da Ajuri Ngelale, kakakin Shugaba Tinubu ya fitar ranar Asabar ta ce shugaban kasar ya amince da gayyatar da shugaban Amurka ya yi masa ta hannun wakilin shugaban kasar da kuma mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka a kan harkokin Afirka Molly Phee.
Mai yiwuwa shugabannin biyu su tattauna a kan rikicin siyasar da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar, inda Shugaba Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS, yake aiki da sauran shugabannin Yammacin Afirka domin shawo kan matsalar.
Tinubu, wanda ya soma aiwatar da manyan sauye-sauye kan tattalin arzikin Nijeriya, ya yi kira ga Amurka ta zuba karin jari a kasar sannan ta karfafa dangantaka ta fuskar kare mulkin dimokuradiyya a Yammacin Afirka, a yayin da juyin mulki ke neman zama abin da ake yayi a yankin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
