Connect with us

News

Kotu ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin gwamnan Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar kano ta tabbatar da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar kano.

 

Kotun Mai alkalai guda karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ce ta tabbatar da hakan yayin zaman sama da awanni 8 ta na’urar zoom.

Akwai Yiwuwar Ta Yanar Gizo Za A Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Kano

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin gwamnan jihar kano, hakan tasa jam’iyyar APC ta garzaya gaban kotu don ƙalubalantar nasarar da Abba Kabir ya Samu.

Advertisement

 

Yayin zaben dai INEC ta ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u Sama da Miliyan 1 yayin da ta ce Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ya Sami kuri’u Sama da Dubu dari takwas.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending