News
Rundunar Sojoji sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da kisan wani malamin addini a Kaduna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar sojin Operation Safe Haven (OPSH) ta bayyana cewa ta kama wasu mutane biyu kan kashe wani malamin addini Stephen Ngophe.
DAILY POST ta rawaito cewa an kashe Ngophe shine a ranar 9 ga Satumba, 2023, a hannun wasu ‘yan bindiga da suka kai hari tare da kona gidan cocin Katolika da ke Kamanton a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Tallafin rage raɗaɗi: Kungiyar SERAP ta maka gwamnoni a kotu kan tallafin N72bn
Kakakin rundunar Operation Safe HavenOPSH, Captain Oya James, wanda ya gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar Rundunar Operation Safe Haven , ya bayyana sunayensu da Ahmed Abdullahi da Hassan Mato.
Ya ce za a mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda da zarar an kammala bincike.
Sai dai Abdullahi ya musanta zargin, inda ya kara da cewa shi bai san da aikata laifin ba.
“Ina gida sai jami’an tsaro suka zo suka kama ni. An kawo ni nan aka hukunta ni mai tsanani ba tare da na aikata wani laifi ba. Ni daga gidan sarauta ne kuma ba zan iya aikata irin wannan laifin ba. Ba a gaya mini abin da na yi ba sai yanzu.” inji Abdullahi
