Connect with us

News

Kungiyoyin Kwadago za su yi taro don fitar da matsaya a kan niyyarsu ta shiga yajin aiki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Shugabannin Kngiyoyin kwadago na kasa za su gudanar da taro da takwarorinsu na rassan kungiyoyin ma’aikata don tattauna batun karin albashin wucin gadi na N35,000 a tsawon wata shida da gwamnatin tarayya ta yi ranar Lahadi ga ma’aikatan tarayya.

 

Advertisement

Shugaba babbar kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Joe Ajaero ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, bayan wani taro na tsawon sa’a hudu da jami’an gwamnati karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar, Mista Femi Gbajabiamila.

Tallafin rage raɗaɗi: Kungiyar SERAP ta maka gwamnoni a kotu kan tallafin N72bn

Kwamared Ajaero ya ce kungiyoyin kwadago su kadai, ba za su iya dakatar da shiga yajin sai-baba-ta-gani da suka tsara farawa daga gobe Talata ba, sai fa idan sun tuntubi rassan kungiyoyin wakilansu.

Advertisement

Wani labarin kuma Tallafin rage raɗaɗi: Kungiyar SERAP ta maka gwamnoni a kotu kan tallafin N72bn

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

Advertisement

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Advertisement

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

 

Advertisement

Ya ce sun gudanar da taro kuma sun duba kusan dukkan batutuwan da ake dambarwa a kansu da kuma alkawurran da gwamnati ta yi, da hanyoyin da za a bi don tabbatar da ganin an cika su.

 

Advertisement

Don haka za mu je, mu kia wa ma’aikatan da muke wakilta wadannan alkawurra kafin zartar da wata sabuwar matsaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending