News
Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Mutum Hudu A Jahar Taraba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yansandan jihar Taraba ranar ta tabbatar da mutuwar wasu mutum hudu sakamakon wutar lantarki a yankin Danyavo da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar litinin.
Bayanai sun yi nuni da cewa, an kawo wuta mai karfi ne a unguwar, lamarin da ya janyo bugawar taransifoma har ya janyo hakan.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Usman, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Jalingo.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin.
Jami’in ya bayyana cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su, sun hada da Remond Ofonbuk, dan shekara 44 a duniya, da matarsa, Mfonbong Remond, Hevean Remong dan shekara 15, da kuma First Remond dan shekara 13.
Usman ya ce, an ajiye gawarwakin mamatan a dakin adana gawarwaki domin gano hakikanin abun da ya janyo tashin gobarar.
Wani labarin kuma Hukumar WAEC ta nada sabon shugaban ta a Najeriya
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
