News
Shehu Sani Ya Yabawa BUA Kan Rage Farashin Siminti, Ya Roki Masu Abinci Su Yi Koyi Da Shi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yabawa mai kamfanin BUA kan rage farashin siminti da ya yi a dai-dai lokacin da ake cikin wani hali.
Kamfanin ya dauki wannan matakin ne yayin da Dala ke kara tashi da kuma halin da ‘yan Najeriya ke ciki a wannan yanayi.
Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a jiya Litinin 2 ga watan Oktoba inda ya ce wannan abin yabawa ne a kasar nan
Sanata Shehu Sani ya yabawa mai kamfanin BUA kan rage farashin siminti zuwa Naira 3,500 a Najeriya.
Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano (PHIMA) ta rufe asibitin Reach
Kamfanin BUA wanda shi ne na biyu a kasar wurin samar da siminti ya ce za a fara siyar da simintin kan sabon farashin daga ranar 2 ga watan Oktoba,
Har ila yau, ya roki masu siyar da kayan abinci da su kwaikwayi hali irin na BUA don rage wa mutane radadin rashin farashin kaya a kasar.
Ya rubuta kamar haka:
“Duk da tashin farashin Dala, BUA ya rage kudin siminti, wannan abin a yaba ne kuma wanda ba a taba ganin irin shi ba. “Mu na fatan wannan ba talle ba ce, ina kira ga masu siyar da abinci su kwaikwayi hali irin na BUA.
Wani labarin kuma Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano (PHIMA) ta rufe asibitin Reach
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
