Connect with us

News

Rundunar Yan sanda A Kano Sun Musanta Zargin Daukar Masu Laifi Aiki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta karyata zargin da ake yi mata na kitsa wani shirin daukar masu laifi aiki da sunan yaki da masu aikata miyagun laifuka a jihar.

 

Sanarwar da Kakakin Rundunar, Abdullahi Kiyawa ya fitar, ta ce, tubabbun ’yan baranda 50 daga cikin 222 da ke haddasa tashe-tashen hankulan siyasa a jihar, amma daga baya suka mika makamansu tare da yin alkawarin ba za su koma ga tada tarzoma ba, su ne aka dauka aiki a sashe na musamman na hukumar ‘yansanda.

Zulum Ya Bayar Da Umarni A Binciki Gawar ‘Yar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Maiduguri

Shima da yake maida martani cikin gaggawa, kwamishinan ‘yansanda na jihar, Mohammad Usaini Gumel, ya caccaki sukar da aka yi wa hukumar kamar yadda ya kafe kan cewa, an horar da masu laifin bayan sun tuba kafin a tabbatar da su a matsayin ma’aikatan hukumar.

Advertisement

Gumel ya shaida wa manema labarai cewa, rundunar ‘yansandan ba ta yi kasa a guiwa ba wajen mayar da tsoffin ‘yan barandan siyasa zuwa sashen hukumar na musamman bisa umarnin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce, amfani da shawarar na da matukar muhimmanci.

Ya ce, gwamnan ya yi amanna da shirin, a maimakon a bar ‘yan barandan su fada hannun miyagun ‘yan siyasa da za su iya amfani da su wajen tayar da fitina.

A wani labarin kuma Zulum Ya Bayar Da Umarni A Binciki Gawar ‘Yar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Maiduguri

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending