Connect with us

News

Bai Kamata A Ce Shugaban Kasa Ne Yake Nada Shugaban INEC Ba  – Farfesa Attahiru Jega

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi wa dokar zabe ta 2022 kwaskwarima.

Ya ce duk da cewa dokar zabe ta kasa ita ce mafi inganci a tarihin kasar, amma ba ta cika ba,kuma akwai bukatar a kara yin gyare-gyare don kawar da shubuha da kuma karfafa wasu sassanta.

Advertisement

Ya Kamata Alumma su maida hankali wajen karfafa guywar masu hidimtawa kungiyoyi

Farfesa Attahiru Jega Ya bayyana hakan ne a wani taron kwana biyu da cibiyar nazarin harkokin dimokaradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya wa sanatoci a garin Ikot Ekpene, jihar Akwa Ibom.

Gyare-gyaren, in ji shi, ya kamata a gyara hanyar lantarki daga zabuka masu zuwa a shekarar 2027.

Advertisement

 

Ya kuma ce, bai kamata shugaban kasa ya sake samun ikon nada shugaban INEC da kwamishinonin hukumar na kasa ba domin kwato hukumar daga bangaranci.

Advertisement

 

Ya ce kamata ya yi a sake duba dokar domin tabbatar da cewa an warware duk wasu batutuwan da suka taso a kan gudanar da zabe tare da yanke hukunci kafin ranar da za a rantsar da su.

Advertisement

 

Masu ruwa da tsaki da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda sashe na 64 na dokar zabe, wanda ya bayyana yadda ake yada sakamakon zaben, na da saukin magudi.

Advertisement

 

Sai dai Jega ya ce ya kamata a fayyace sashen ta hanyar wajabta watsa sakamakon zabe, gami da dora sakamakon matakin zabe da takardar sakamakon da ake amfani da shi a matakai daban-daban na tattara sakamakon zabe.

Advertisement

 

“INEC za ta samu isasshen lokacin da za ta shirya aiwatar da wannan, idan an yi wa dokar kwaskwarima da wuri a zaben da ke tafe,” in ji shi.

Advertisement

 

Ya kuma yi kira da a bullo da yanayin fara kada kuri’a ga wadanda suka cancanci kada kuri’a, kamar ma’aikatan INEC, masu sa ido da direbobinsu, jami’an tsaro, da ‘yan jarida ko kuma wani tsari na musamman da zai ba su damar kada kuri’a a ranar zabe, musamman zaben shugaban kasa.

Advertisement

 

Tsohon shugaban na INEC ya bayar da shawarar cewa ‘yan kasashen waje su kada kuri’a, musammam zaben shugaban kasa, don bai wa ‘yan kasa damar kada kuri’a, musamman wadanda ke aiki a kasashen waje.

Advertisement

 

Ya ce, “Akwai bukatar a sanya tsauraran sharudan janyewar dan takara da kuma maye gurbinsa don hana cin zarafi. Ba wa INEC damar tantancewa da kuma idan ya cancanta ta haramta wa ‘yan takarar da shaidarsu ta nuna cewa ba su cancanta ba.

Advertisement

 

“Akwai bukatar doka ta ba wa ‘yan takara da ke wajen jam’iyyun siyasa dama, da kuma ‘yan kasa masu biyan haraji su shigar da kara a kan ‘yan takarar da ke bai wa INEC bayanan karya game da takararsu.

Advertisement

 

“Duk da cewa sashe na 132(8) & (9) ya bayar da wa’adin da kotuna da kotunan daukaka kara za su yanke hukunci, akwai bukatar musamman dangane da zababbun mukaman zartarwa, a tabbatar da an warware dukkan shari’o’i da kuma yanke hukunci a gabanin. ranar rantsuwa.

Advertisement

 

“Bincika tsarin nade-naden mukamai a INEC, musamman don karfin shugaban kasa wajen nada shugaban INEC da kwamishinonin INEC na kasa, domin kubutar da hukumar daga mummunan zato da ake maga.

Advertisement

 

“Ya kamata a samar da ka’idoji don gabatar da koke-koke ga duk wan

Advertisement

da aka zaba yayin wannan aikin.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending