News
Wasu karin mutane biyu sun mutu a hannun ‘yan ta’adda a yankin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu karin mutane biyu sun mutu a hannun ‘yan ta’adda a yankin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.
Rahotanni sunce ‘yan ta’addan sun yi harbi ne kan mai uwa da wabi inda suka raunata wasu mutum uku a madatsar ruwan Bagoma, kofar birni zuwa garin Birnin-Gwari daga jihar Neja.
Yan Majalissar Dokoki Suna Maida Martani Ga Masu Sukar Shirin Sayen Motocin Alfarma
Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai dan Bijilante da kuma wani dan gudun hijira daga yankin Dagara.
A cewar shugaban kungiyar rajin samar da tsaro da shugabancin na gari a Birnin-Gwari Ibrahim Abubakar, lamarin ya faru ne daf da sallar magariba a gidan main a KBY dake Dam Bagoma.
Ya ce wasu mutane uku sun samu raunuka daban-daban yayin da ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da wasu da dama.
A Wani labarin kuma Yan Majalissar Dokoki Suna Maida Martani Ga Masu Sukar Shirin Sayen Motocin Alfarma
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
