News
Mashako: Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya Gargadi Jama’a kan Shirya Taruka Barkatai
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamishinan lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya yi kira ga jama’a da su guji tarukan da ba su dace ba domin kare kansu da sauran jama’a daga kangin cutar mashako.
Dakta Labaran ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga Sashin Hulda da Jama’a na ma’aikatar da aka raba wa manema labarai, ciki har da Jaridar Inda Ranka.
Hukumar INEC Ta Kare Karin Kasafin Kudi Na Biliyan 18 A Majalisar Dokokin Tarayya
Wannan, a cewar sanarwar, cigaba da wayar da kan jama’a ne kan wajibcin daukar matakan kariya ga kowa da kowa da nufin dakile yaduwar cutar mashako a jihar Kano.
Kwamishinan ya ce cutar mashako cuta ce da iska ke yadawa, don haka duk mutumin da ake zargin ya kamu da cutar ko kuma yana da alamun cutar mura mai tsanani, lallai irin wannan mutumin a hanzarta ware shi sannan a kai shi asibiti.
Ya jaddada cewa kada wannan mutumin ya yi cudanya da lafiyayyun mutane yana tari, atishawa da yin musabaha da mutane, yana mai nuni da cewa wadannan su ne manyan hanyoyin yada cutar.
Dakta Labaran ya ba da shawarar cewa idan yaro ne ya kamu da cutar, kada iyayensa su bar shi ya je makaranta, su gaggauta kai shi asibiti don ya samu kulawar da ta kamata ta hanyar gudanar da gwaje-gwajen da suka dace don sanin ko akwai cutar mashako ko babu, yana mai tabbatar da cewa yin hakan zai taimaka matuka wajen dakile yaduwar cutar a tsakanin sauran yara.
Kwamishinan ya gargadi mutane da su daina hada taruka marasa amfani musamman ganin yadda ake fuskantar shigowar yanayin sanyi, lokacin da cutar mashako ke kara ta’azzara.
Ya kara da cewa idan taron ya zama wajibi, to kada a yi shi rufaffen wurin babu isasshiyar iskar shaka, yana mai ba da shawarar cewa ya kamata a yi taron a budadden wuri tare da kiyaye amfani da abin rufe fuska, domin yana taimakawa wajen tace kwayoyin cutar da mutum zai iya shaka.
Dakta Labaran ya bayyana cewa, babbar hanyar kariya daga cutar mashako ita ce allurar rigakafi, ya mai kira ga iyaye da su tabbatar an yi wa ‘ya’yansu masu shekaru tsakanin 4 zuwa 14 cikakken allurar rigakafin sau uku a jere, daya bayan kowane mako hudu, domin jikinsu ya samu cikakkiyar kariya.
Dakta Labaran ya karkare da cewa, idan har aka tabbatar da cewa yaro ya kamu da cutar mashako, dole ne a yi wa dukkan ‘yan uwansa allurar rigakafi ba tare da la’akari da shekaru da jinsinsu ba, ya kara da cewa ko makwabtansu ma sai an yi musu allurar rigakafin don kar su kamu da cutar ta mashako.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
