News
Yadda Kanawa Suka Tarbi Abba Bayan Hukuncin Kotun Daukaka Kara
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Daruruwan al’ummar Kano ne suka yi dafifi a yammacin ranar Litinin, don tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf da kotun daukaka kara ta kora, inda suka nuna alhininsu tare da yi masa addu’ar samun nasara a kotun koli.
Jama’a jihar sun mamaye titunan birnin Kano, inda suka yi ta fito daga shagunansu da gidajensu domin nuna goyon bayansu ga gwamnan da ya kai ziyara domin gudanar da ayyuka a cikin birnin.
Majalissar Wakilai Na Bincike Kan Yadda Hukumomi Suka Kashe Naira Billiyan 447.6 Lokacin Corona
Yusuf, ya bayyana ne bayan da kotun daukaka kara da ke Abuja ta kore shi, magoya bayansa ne suka tarbe shi daga gidan gwamnati zuwa Asibitin kwararru na Murtala da ke cikin garin Kano a yammacin ranar Litinin.
Jama’a sun mamaye tituna suna rera wakoki da jinjina tare da yi masa addu’a.
Leadership ta ruwaito cewa kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar 17 ga watan Nuwamba, ta sake tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta kori Gwamna Yusuf tare da bayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin zababben gwamnan jihar.
Jama’ar da suka fito domin tarbar sa suna ta rera wakokin “Kano sai Abba, hudu sau hudu” (Kano ta Abba ce).
Gwamna Yusuf ya kaddamar da sashen bada agajin gaggawa na asibitin kwararru na Murtala Mohammed, daya daga cikin ayyuka da dama da ya fara tun bayan da aka zabe shi.
Kazalika, ya duba a jihar a yammacin na ranar Litinin.
A wani labarin kuma Majalissar Wakilai Na Bincike Kan Yadda Hukumomi Suka Kashe Naira Billiyan 447.6 Lokacin Corona
Uwar gidan tsohon shugaban Amirka, Michelle Obama ta shaida wa BBC cewa yara da dama a duniya na fuskantar matsalar auren wuri, lamarin da bai kamata a kauda kai ba.
Mrs Obama na magana ne lokacin ziyarar da ta kai Malawi, ƙasar da ake aurar da kashi 42 cikin 100 na ‘yan mata da ba su kai shekara 18 ba.
Ta ce “bai kamata mu kauda kai kan wannan batun ba,matukar za a tattauna kan wasu batutuwan na daban. Sauyin yanayi, da Talauci da yake-yake na daga cikin dalilan auren wuri.
MDD ta yi kiyasin cewa ana aurar da mata miliyan 12 a kowacce shekara, waɗanda ba su kai shekara 18 ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
