Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Zata Karya Farashin Makamashin Iskar Gas A Fadin Kasar Nan 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta bullo da wani tsari na inganta samar da Mamakashin iskar gas a fadin kasar nan, a wani mataki na magance matsalolin da suka shafi samar da makamashin da ake amfani das hi wajen yin girki.

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti wanda aka dorawa alhakin bada shawarwari kan yadda za’a inganta samar da makamashin iskar gas din, da kuma karya farashinsa a cikin kasa da mako daya.

Advertisement

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Ba Wa Falasɗinawa Naira Miliyan 100

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin karamin ministan Man fetir na kasa, Ekperikpe Ekpo ya fitar.

Sanarwar ta Ambato karamin ministan Mai na baiyana daukar wadan nan matakai biyo bayan tashin farashin makamashin Gas zuwa sama da naira 1 da 100 a wasu sassa na kasar nan, daga naira 700 da ake siyar dashi kan kowane Kilogiram daya.

Advertisement

A wani labarin kuma Sheikh Dahiru Bauchi Ya Ba Wa Falasɗinawa Naira Miliyan 100

Kakkarfar guguwa haɗe da ruwan sama sun afka kudancin ƙasar Ukraine, lamarin da aka jima ba a gani ba cikin shekaru ayankin tekun Baharul Aswad.

Advertisement

Kusan mutane dubu biyar da ke zaune a yankin Crimea da Rasha ta mamaye na zaune babu wutar lantarki, bayan guguwar ta karya manyan bishiyoyin da suka faɗa kan turakun wutar lantarki.

Guguwar ta kuma janyo ambaliyar ruwa a kauyuka da garuruwan da ke kusa, an kuma kwashe mazauna garin Sebastopol bayan ambaliyar da kogin yankin ya yi.

Advertisement

Hotunan da aka yaɗa a intanet sun nuna biranen Bed-yansk da Mariupol da tekun Azov duk sun mamaye da ruwa.

A can yammacin birnin Odesa ma lamarin ya munana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending