Connect with us

News

Kotun Koli Ta Ce A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Takardun Kudi Har Sai Sabin Da Hali Ya Yi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Kotun Kolin Najeriya ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira har sai sabin da hali ya yi.

A zaman Kotun Kolin na ranar Laraba, Mai Shari’a John Okoro wanda ya jagoranci sauran alkalai shida, ya ce babu ranar daina amfani da tsofaffin takardun kudaden da CBN ya sauya wa fasali.

Advertisement

Godwin Emefiele Zai Yi Bukin Kiristimeti Da Sabuwar Shekara A Gidan Gyaran Hali 

Ya kara da cewa za tsofaffin kudaden za su ci gaba aiki kafada-da-kafada da sabbabbin da aka yi, har sai lokacin da bankin CBN ya gama maye gurbin tsofaffin da sababbi da kuma cika ka’idojin da suka kamata.

Mai Shari’a John Okoro ya ce, “tsofaffin N200, N500, da N1000 naira za su rika aiki tare da sabbin da aka yi har zuwa lokacin har zuwa lokacin da gwamnati ta yanke shawarar daina amfani da tsofaffin bayan ta tuntubi masu ruwa da tsaki da kuma tanadar duk abubuwa da suka kamata.”

Advertisement

Kotun Kolin ta yanke hukuncin ne baya karar da Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Kasa, Lateef Fagbemi (SAN), ya shigar na neman kotun ta soke wa’adin ranar 31 ga watan Disamba 2023 na daina amfani da tsoffin takarduna N200 da N500 da kuma N1,000.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ne ya kawo batun sauyin takardun kudin da kuma takaita cirar tsabar kudi, gabanin zaben 2023, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

Advertisement

Duk da umarnin kotu na hana sauyin kudin, CBN na shirin dakatar da amfaninsu a ranar 31 ga watan Disamba, daga bisani ta ce za a ci gaba da amfani da su, zuwa lokacin da za ta kammala tuntubar masu ruwa da tsaki kan matakin da kuma shirinta na zuwa kotu domin samun izinin soke wa’adin na 31 ga wata Disamba.

A wani labarin kuma Godwin Emefiele Zai Yi Bukin Kiristimeti Da Sabuwar Shekara A Gidan Gyaran Hali 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending