News
Matashi ya kashe kansa bayan ya yi asarar Naira miliyan 2.5 a cacar yanar gizo
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani mutum mai shekaru 31 ya kashe kansa a jihar Abia, a kudu maso gabashin Najeriya, bayan da aka ce ya yi asarar Naira miliyan 2.5 a cacar yanar gizo.
Mutumin mai suna Chukwuma Onoh, an ce ya ciyo bashin Naira miliyan 1.2 daga hannun abokansa inda ya hada da na sa Naira miliyan 1.3 don yin buga cacan amma bai ci ba.
” Zaɓin da ya rage min shine kawai in kashe kaina domin ba zan iya muamula cikin jama’a ba bayan irin wannan abin kunya da ya same ni, sannan kuma ta ina zan samu kuɗin biyan bashin da na ci na buga wannan caca.” Wannan shine saƙon da muka gani wanda mutumin ya saka a WhatsApp.
Matashin ya rika rubuta wa a shafin sa ta Facebook cewa shi zai kashe kansa saboda ya gaji da rayuwar duniya sannan bai san ta inda zai fara neman kuɗi ya biya masu bashi ba.
Ko da ya je siyan maganin kashe kwari ‘Sniper’ sai da ya rubuta a Facebook cewa ” Ga ni nan zan siya maganin kashe kwari zan sha in koma ga mahalicci na. Ba zan iya jure wa wannan hasara da na yi ba.
Ko da abokanan sa suka yi kokarin cimma sa, sun iske ya kwankwaɗi ruwan maganin har ya fara shureshure.
Premium Times ta ruwaito cewa Likitoci a asibiti sun tabbatar da ya sheka lahira, a lokacin da suke kokarin ceto sa.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News12 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
