Connect with us

News

Gwamnatin Zamfara Ta Nemi A Hukunta Wacce Ake Zargi Da  A Zabtar Da Yarinya ‘Yar Shekara 12 Da Wuta.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal, ta dau alwashim hukunta Aisha Tsafe da aka kama da azabtar da yarinya ‘yar shekara 12 da wuta.

Advertisement

An rahoto cewa, Aisha Tsafe ta kona leda a wuta ne sannan ta daukota ta na diga wa yarinyar a bayanta.

Hukumar NAHCON Ta Dakatar Da Rabon Kujeru Ga Kamfanonin Jirgin Yawo

Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar, Dakta Nafisa Muhammad, ta tabbatar da matakin Gwamnati na hukunta Matar wacce aka ce kishiyar Uwar Yarinyarce, a yayin da ta ziyarci yarinyar mai suna Safiya Tsafe.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa Dakta Nafisa Muhammad tayi kira da babar murya kan a hukunta Aisha Tsafe da ta azabtar da diyar kishiyar ta ‘yar Shekaru 12 Safiya.

Jami’in yada labarai na Ma’aikatar mata da Jindadin al’umma, Suleman Isa ne ya bayyana haka a takardar da ya sanyawa hannun ga manema labarai a Gusau.

Advertisement

Tun da farko, mahaifiyar Safiya, Malama Maryam Muhammad, ta roki gwamnatin jihar da kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka wajen bin hakin diyarta, Safiya.

Mahaifiyar Safiya ta gode wa Kwamishiniyar da wasu jami’an kungiyoyi masu zaman kansu da suka nuna damuwa kan abin da ya faru da ‘yarta.

Advertisement

A wani labarin kuma Hukumar NAHCON Ta Dakatar Da Rabon Kujeru Ga Kamfanonin Jirgin Yawo

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending