Connect with us

News

Babbar Magana: Ƙasar Jamus Ta Kirkiro Injin Kyankyasa Jarirai. 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Kasar Jamus ta kirkiro wani inji da zai rika raino tare da kuma kyankyasar jarirai irinsa na farko a duniya.

Sunan injin ‘Ecto Life’ kuma zai samar da duk wani abu da jariri yake bukata a cikin mahaifiyarsa har ma da kari.

Kungiyar Dalibai Ta Yabawa Gwamnati Kan Cire Manyan Makarantu Daga Tsarin Biyan Albashi Na IPPIS

An shafe sama da shekara 50 ana kirkirar wannan injin, wanda manyan likitoci da masana suka yi dafifi wajen tabbatuwarsa.

Injin zai iya kyankyasar jarirai 30,000 a cikin shekara guda.

Advertisement

A cewar wanda ya kirkiri injin a birnin Berlin na Kasar Jamus, Hashem Al-Ghaili, injin zai kawo karshen matsalolin da mata ke fuskanta yayin daukar ciki, musamman masu fama da ciwon daji wanda likitoci suka ce ba za su sake haihuwa ba.

Kazalika, injin zai kawo mafita ga matan da ke mutuwa wajen haihuwa, matan da ake yi wa tiyata yayin haihuwa, matan da ke yawan barin juna biyu da sauransu.

Injin Ecto Life da zai rika kyankyasar jarirai,

Injin zai taimaka wa kasashen da yawansu ke raguwa, irin su Japan da Bulgeria da kuma Koriya Ta Kudu ta hanyar haifa musu yara masu yawa.

Ecto Life zai bayar da dama ga iyaye su koyawa jaririnsu irin yaren da suke so su tashi da shi tun suna ciki.

Babban abin da ya fi daukar hankalin duniya game da ‘Ecto Life’ shi ne za a iya zabar wa jariri yanayin hallitar da ake so ya zo duniya da ita, misali za a zabar masa launin fata, yanayin ido, gashi da sauran yadda ake so sassan jikinsa su kasance.

Advertisement

Har wa yau, za a iya amfani da injin wajen kara kaifin basirar jariri.

A cewar Al-Ghalil, Ecto Life zai bai wa jarirai kariya daga kamuwa da cututtukan da suke kamuwa a lokacin da suke cikin iyayensu mata.

Sai dai Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa tambaya a nan shi ne, duniya za ta karbi wannan injin ta rika amfani da shi, idan har hakan ta kasance, mece ce makomar iyaye ke nan wajen haihuwa?

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending