Connect with us

News

Najeebah: Yadda kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa wata matashiya ya tayar da hankali a Nijeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Yan Nijeriya sun soma matsa lamba ga rundunar ‘yan sandan kasar bayan wasu rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mutane sun kashe daya daga cikin ‘yan mata shida da suka kama a kan hanyarsu ta komawa Abuja daga Kaduna.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa an sace Najeebah da mahaifinta da ‘yan’uwanta ne ranar 9 ga watan Janairun da muke ciki.

Da Dumi-Dumi: Abba Gida-gida Ya Nada Kwankwaso, Ganduje, Shekarau, Mukami A Kano

Sai dai daga bisani sun saki mahafin nasu sannan suka bukaci a biya su naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa kafin su saki ‘yan matan.

Advertisement

Tun daga lokacin ne wata makusanciyarsu mai suna Asiya Adamu ta kaddamar da kamfe a shafukan sada zumunta musamman shafin X, wanda a baya ake kira Twitter, tana neman mutane su taimaka su hada kudin domin kai wa ‘yan bindigar, wadanda suka yi barazanar kashe su.

Sai dai ranar Asabar Asiya ta wallafa sako da ke cewa ‘yan bindigar sun kashe Najeebah.

Advertisement

Shi ma Farfesa Isa Ali Pantami, tsohon minista a Nijeriya, ya tabbatar da kisan Najeebah a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

“Yanzu na karanta labarin kisan ‘yarmu Najeeba (daliba ‘yar aji 400 a ABU). Na yi magana da mahaifinta game da sauran ‘ya’yanmu biyar da aka yi garkuwa da su. Allah ya gafarta mata, ya kubutar da sauran ‘yan matan sannan ya kawo zaman lafiya a Nijeriya,” in ji Pantami.

Advertisement

Neman Dauki

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin ‘yan kasar inda suka rika yin kiraye-kiraye ga rundunar ‘yan sandan kasar ta kubutar da sauran ‘yan matan da ke hannun masu garkuwa da mutane.

Advertisement

Malam Bashir Ahmad, mai taimaka wa tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kan shafukan sada zumunta, na daya daga cikin wadanda suka ja hankalin rundunar ‘yan sandan kasar game da wannan batu.

Ya wallafa sako a shafinsa na X inda ya roki rundunar ta yi gaggawar tsoma baki a lamarin tare da kubutar da sauran ‘yan matan bayan “masu garkuwa da mutane sun kashe Najeebah a matsayin gargadi sannan suka bukaci a biya N100m a matsayin kudin fansa na sauran wadanda aka yi garkuwa da su”.

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ya ce suna bibiyar batun satar ‘yan matan amma “muna bukatar wasu bayanai. Ya kamata ‘yan’uwan (matan da aka sace) su yi magana da ni kai-tsaye, su tura mini sako.”

Adejobi ya ce “za mu yi bakin kokarinmu don daukar matakan da suka dace wajen ganin an kubutar da su ba tare da ko kwarzane ba.”

Advertisement

Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta yi kaurin suna wajen yin garkuwa da mutane. Sai dai lamarin ya lafa a watannin baya bayan nan, ko da yake yanzu masu bin hanyar sun ce an samu karuwar garkuwa da mutane.

 

Advertisement

TRT Afrika

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending