News
Mota ta take wani matashi bayan da ya kwaci wayar wata mata zai tsallaka Titi a jihar Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da samun rahoton wani matashi da ya zare Dan bida ya kwaci wayar wata mata a yankin gidan Zoo a jihar, yana tsallaka titi mota ta takeshi.
Gidan Radiyo Dala Fm ta ruwaito cewa Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Abdulahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta da yammacin Lahadin nan.
Kiyawa ya ce ya samu rahoton faruwar al’amarin inda aka nemi daukinsu domin su kai matashin Asibiti.
A wani labarin kuma AFCON 2023: Nijeriya Ta Buga 1-1 Da Kasar Equatorial Guinea
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
