Connect with us

News

Wasu ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Farmaki Ofishin ‘Yansanda A Jihar  Katsina

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi sun kai hari ofishin ‘yansanda, tare da kashe dan sanda guda daya a kauyen Saki Jiki da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Leadership ta ruwaito cewa Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abubakar Aliyu Sadiq, a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wani dan sanda ya samu rauni a harin, ba ya ga wani daya da ya rasu.

Advertisement

Kotun koli ta tabbatar da Abdullahi Sule a matsayin gwamnan Nasarawa.

Sadiq, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis, kuma tuni ‘yansanda suka dakile harin.

Ya ce, “A jiya (Alhamis) da misalin karfe 8 na dare wasu ‘yan bindiga sanye hijabi, suka farmaki ofishin ‘yansanda da ke kauyen Saki Jiki a Karamar Hukumar Batsari.

Advertisement

“Jami’an sun yi artabu da su kuma sun yi nasarar dakile harin. Sai dai jami’i daya ya rasa ransa sannan wani ya samu rauni sakamakon harin.

“Za a sanar da ci gaban da aka samu nan gaba.”

Advertisement

Karamar hukumar Batsari dai na fuskantar sabbin hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan.

A cikin mako guda, ‘yan bindiga sun kai hari biyu a yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending