News
Tsadar Rayuwa: Babangida ya gargadi Shugaba Tinubu kan yiwuwar juyin mulkin soja a Najeriya?
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Rade-radin cewa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya gargadi Shugaba Tinubu game da juyin mulki ba gaskiya Sai dai, akwai shafukan sada zumunta na kwaikwayo mai dauke sunan tsohon shugaban mulkin sojin da ke yada batun juyin mulkin Da yawa daga cikin masu bibiyar shafukan na kwaikwayo basu duba don bambance ko shafin da gaske na tsohon shugaban ba ne
Library Radio ta rawaito cewa Shugaba Bola Tinubu na shan suka game da matsin tattalin arziki da aka shiga tun bayan da sanar da matakin cire tallafin mai da karya darajar naira. Matakan da shugaban ya dauka tun bayan rantsar da shi sun janyo hauhawar farashin kayayyaki abinci da sauran bukatun yau da kullum, kuma masu ruwa da tsaki, ciki har da ‘yan adawa da shugabannin kwadago, suna ta kira kan janye matakan.
Shugaba Tinubu yayi wata muhimmiyar ganawa da Dangote, BUA, Elumelu, da sauran su
Sannan, an yi zanga-zanga a wasu jihohi a kasar saboda tsadar rayuwa. Jihohin da aka yi zanga-zanga sun hada da Oyo, Cross Rivers, Niger da Kano. Tsadar rayuwa: Yan Najeriya sun bukaci sojoji su yi juyin mulki Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jin dadinsu a shafukan sada zumunta saboda halin da ake ciki, yayin da wasu ke neman sojoji su yi juyin mulki. Wani a shafin X (Tuwita), @General_Ibbro (Ibrahim B. Babangida), ya sha bayyana ra’ayinsa kan yiwuwar cewa sojoji za su yi juyin mulki ga gwamnatin Tinubu.
Ga abin da ya rubuta: “Ba na goyon bayan juyin mulki, amma ina kira ga gwamnatin tarayya da ta dubi halin da ‘yan kasar ke ciki, su kawo dauki kafin abin ya zama annoba.”
Wani shafin YouTube ya yayata maganar bayan fadar ta a wani shiri, in da ta bayyana maganar a matsayin abin da Babangida ya ce.
Tinubu ya yi zancen mayar da tallafi da soke karya naira saboda shiga kuncin rayuwa
GASKIYAR BATUN JUYIN MULKIN BABANGIDA
Babu wata alama da ke nuna cewa tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), da ya mulki Najeriya daga 1985 zuwa 1993 ne ya fadi maganar. Kuma, shafin X din ya fi kama da na bogi kuma babu shaidar tsohon shugaban kasar a rubutun. Sai dai, da yawan ‘yan Najeriya da ke martani a rubutun ba su duba ko shafin gaskiya bane, dalilin da ya sa ake tunanin Babangida ne. Wani bincike ya kuma bayyana cewa a bude shafin a shekarar 2013 kuma ana gudanar da shi daga Minna, babban birnin Jihar Niger, kuma a nan ne gidan Babangida ya ke.
