Connect with us

News

‘Yan sanda sun kama mutum hudu dake safarar yara kanana a Kaduna

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’an ta sun kama wasu mutane hudu dake safarar yara kanana a jihar.

Advertisement

Jami’an tsaron sun kama Shehu Sani mai shekara 40, Tskan Isiaku mai shekara 43 da Hafsat Hussaini ‘yar shekara 24 duk dake suna zama a Ungwar Rimi a karamar hukumar Kaduna ta Arewa sannan da Angela Onazu dake zama a unguwar Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun.

Yadda Gayyatar Da Jami’an Tsaro Suka Yi Da  Sheikh Gumi Ta  Gudana

Kamen da dakarun suka yi ya faru bayan sa’o’I 24 da dakarun suka kama wani sojan karya mai suna Ya’u Ja’afar dake damfarar mutane da kuma yi musu fashi da makami jihar.

Advertisement

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Mansur Hassan ya ce mutanen sun tabbatar wa jami’an tsaron cewa suna safarar yara kanana sannan dakarun sun ceto wata karamar yarinya mai suna Zainab mai shekara biyu daga hannun su.

Hassan ya ce mutanen sun yi bayanin cewa sukan kama yara kanana dake gararamba a titi da wadanda aka aike su su kadai ba tare da wani babba tare da su ba.

Advertisement

Ya yi kira ga iyaye da su rika sa ido suna kula da shiga da fitan ya’yan su domin kare su daga fadawa hannun mutane irin haka.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ali Audu Dabigi ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da kokarin wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending