Connect with us

News

Idan Isra’ila ta kaiwa Iran hari babu ruwanmu a ciki – Amurka

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A yayin da Isra’ila ke nazarin yadda za ta mayar da martani kan harin da Iran ta kai a karshen mako, Amurka ta bayyana cewa babu ruwanta idan har kasar ta zabi daukar fansa ta hanyar soji.

Sakon na Amurka da ba a saba ganin irinsa kan babbar aminiyarta da take bawa taimakan soji fiye da kowacce kasa a duniya, ta ce ba za ta shiga rikicin Iran da kuma Isra’ila ba.

Ana Hasashen Cewa Ambaliyar Ruwa Za Ta Shafi Jihohin Nijeriya 31 a daminar bana

Bayan watanni da Isra’ila ta yi na daukar fansa a Gaza, duk da suka daga Amurka da sauran kawayenta da ke cewa ayyukan sojanta sun wuce gona da iri, gwamnatin Biden ta bayyana karara cewa, tana tsoron yaki mafi girma ya barke a Gabas ta Tsakiya.

Mun yi imanin Isra’ila na da ‘yancin daukar mataki don kare kanta, amma wannan wani salo ne na siyasa,” in ji wani babban jami’in fadar White House ga manema labarai jim kadan bayan kawo karshen harin na Iran. ”

Radiyo Faransa ta ruwaito cewa da  wani dan jarida ya tambaye shi ko Amurka za ta taimaka wa Isra’ila wajen tunkarar hare-haren soji, nan take ya bashi amsar cewa a’a.

Advertisement

Amurka ta ce tuni ta isar da wannan sakon kai tsaye ga manyan jami’an Isra’ila a wata ganawar sirri ta wayar tarho da ta gudana tsakanin sakataren tsaro Lloyd Austin da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant.

Harin da Iran ta kai kan Isra’ila da yammacin ranar Asabar ya sha kakkausar suka daga shugabannin duniya, ciki har da jami’an Amurka wadanda da farko suka yi tunanin kasar ta yi amfani da makamai masu linzami guda goma sha biyu ne kacal.

Harin dai, Iran ta kira shi a matsayin ramuwar gayya bayan harin da Isra’ila ta kai ofishin jakadancinta da ke Damascus na kasar Syria.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending