Connect with us

News

Al’ummar Mazabar Gobirawa Na Cikin Matsanantiyar Damuwa Akan Tsayawar  Aikin Fadada Asibitocin  3

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Al’ummar Mazabar Gobirawa na cikin matsanantiyar damuwa tare da bayyana korafin su kan yadda aikin fadada Asibitoci guda 3 ya tsaya cik wanda wakilin Dala a majalisar Dokokin jihar Kano Hon. Lawan Hussain ke gudanarwa a mazabar su ta Gobirawa tun bayan kammala aikin da kimanin kaso 65 wanda ake zargin masu yin aikin da Jan kafa.

Korafin na zuwa ne tabakin daya daga cikin jagororin yankin Comrade Murtala wanda shine Diraktan dake lura da Kafar sada zumunta ta zamani a karkashin KUNGIYAR FITILAR AL’UMMAR GOBIRAWA a zantawar da yayi da manema labarai kan aiyukan da Kungiyar tasa a gaba zuwa karshen shekarar 2024.

Kungiyoyin Da Ke Doka Gasar Premier Za Su Kaɗa Ƙuri’a Kan Bukatar Soke Na’urar VAR

Comrade Murtala ya zargi wanda suke gudanar da aikin fadada Asibitoci da daina zuwa gurin aikin baki daya tare da kwashe kayan su a wasu daga cikin asibitocin.

Murtala ya bayyana asibitocin guda 3 da ayyukan su ya tsaya kamar haka:

Asibitin Gidan Dagacin Gobirawa, Asibitin Tudun bojuwa sai Asibitin Umma Zariya dake Unguwar Filin Durimi inda ya bayyana tasiri da gudun mawar da aikin zai kawo ta fuskar lafiya idan an kammala a yankin.

Advertisement

A karshe ya godewa Dan majalisar a madadin Al’ummar mazabar Gobirawa dangane da kokarin da yayi na kawo irin Wannan aiki har gudu uku a cikin kankanin lokaci tun bayan komawarsa majalisa a karo na biyu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending