News
Iska Mai Karfin Gaske ta Lalata Gidaje Da Dama Da Wuraren Kasuwanci A Nasarawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni na nuni da cewa Gine-gine da dama ne da wuraren kasuwanci iska mai karfin gaske ta lalata dare da dai-dai ta wasu al’ummomi a Lafia dake jihar Nassarawa.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da wasu mazauna Garin Lafia dake Unguwar bayan Command Secondary School.
Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso za su kafa sabuwar kungiyar da suka kira AES
Wani da lamarin ya shafa, Muhammad Iliyasu Garba dan Jarida ne dake aiki da Breeze FM,wani gidan Rediyo mai zaman kansa a Lafia, Yace iska ta yi awon gaba da gidan sa baki daya.
Haka zalika ya kara da cewa rasa madafa dan haka yake Kiran tallafi daga hukumomi da Masu aikin jin Kai a jihar da su kai musu dauken gaggawa.

Garba yace yayi matukar kaduwa game da iftila’in a yayin sabon rufin gidan gugawar ta ya yi gaba daya
Haka zalika lamarin ya shafi makarantar koyon sana’a da fasaha ta Isa Mustapha Agwai inda gine-gine da dama na makarantar abin ya shafa
Muktar Wakeel Daraktan harkokin labarai na makarantar ta cikin wata sanarwa da ya raba manema labarai, yace akalla gine-gine biyar abin ya shafa sosai bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Lafia.

-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
