Connect with us

News

Ya kamata a bar ƴan Najeriya su ɗanɗana kuɗarsu – Buba Galadima

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A ranar 29 ga watan Mayun 2024 ne Najeriya za ta, cika shekara 25 da komawa kan turbar dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba, wadda kuma ake kira Jamhuriya ta Huɗu.

Advertisement

An shiga jamhuriya ta huɗu ne tun daga lokacin da aka rantsar da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayun 1999, abin da ya sa har yanzu ba a kuma samun juyin mulki ko wata tangarɗa ba a tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.

Ronaldo Zai Fafatawa Portugal Wasa A Euro Na Shakarar 2024

Albarkacin wannan rana ne kuma BBC ta fara bin diddigin cigaba ko koma-bayan mulkin na dimokuraɗiyya a ƙasar da ke yammacin Afirka, ta hanyar tattaunawa da shugabannin al’umma, da ‘yan siyasa.

Advertisement

Ɗaya daga cikin irin waɗannan ‘yan siyasa shi ne Buba Galadima, dattijo mai shekara kusan 75 wanda ya fara gwagwarmayar siyasa tun daga shekarar 1978.

Jigo ne a jam’iyyar adawa ta NNPP, wadda tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023.

Advertisement

Kamar yadda aka saba a matsayinsa na ɗan’adawa, Buba Galadima ya caccaki gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, wadda aka rantsar ranar 29 ga watan Mayun 2023 bayan samun nasara a zaɓen watan Fabrairu.

Buba Galadima ya ce tun kafin lokacin babban zaɓen Najeriya na 2023, a matsayinsu na ƴan adawa sun gargaɗi ƴan Najeriya kan zaɓen shugaban da ke ci a yanzu, sai dai al’umma ba su saurare su ba.

Advertisement

Da alama dai Buba Galadima na bayani ne a kan halin da ƙasar ta Najeriya ke ciki a yanzu, inda al’umma ke fama da tsadar rayuwa sanadiyyar matsalar tattalin arziƙi.

Rayuwa ta yi tsada a ƙasar ta Najeriya tun bayan da shugaba Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur, kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi.

Advertisement

Haka nan darajar naira ta ci gaba da faɗuwa idan aka kwatanta da dalar Amurka. Sai dai gwamnatin Tinubu na cewa tana yin hakan ne domin gyara tattalin arziƙi ta yadda zai amfani al’umma a gaba.

Amma Buba Galadima ya ce “a bari su (ƴan Najeriya) ɗanɗana, su ji a jikinsu”.

Advertisement

A cewarsa hakan zai zamo darasi ga al’ummar Najeriya a lokacin zaɓe mai zuwa.

Ya ce za a iya gyara halin da Najeriya ke ciki ne kawai idan mutane sun cire kwaɗayi tare da yin abubuwan da suka kamata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending