News
Jami’an Hukumar Kwastom 2,500 Na Karbar Horo Kan Shirin Zamanantar Da Kasuwanci Na TMP
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jami’an hukumar kwastom na hukumar hana fasa kwauri ta kasa ne zasu samu horo a farkon shekerar 2025 domin tafikar da shirin zamanantar da kasuwanci na hukumar.
Shirin na zamanantar da kasuwanci na hukumar Kwastom tsari ne na fadar shugaban kasa da zai taimakawa wajen manufar bunkasa tattalin arzikin Najeriya a bangarorin da ba na mai ba.
Kungiyar SERAP tayi Allah wadai da kashe N21b wajen Gina ma Kashim Shettima gida
Shirin zai bunkasa ayyukan hukumar hana fasa kwauri da suka hada da kara yawan kudaden shiga da kula da ci gaban kasuwanci da rage ayyukan cin hanci da rashawa da kuma sanya tsarin ya zama mai dogon zango. Ana tsammanin shirin zai haifar da Da mai ido ga ci gaban tattalin arzikin kasarnan.
Ana aiwatar da shirin ne karkashin hadin gwiwa tsakanin Gwamnati da bangarori masu zaman kansu wanda ake kira PPP. Inda aka cimma yarjejeniyar jinginarwa a ranar 30 ga watan Mayu na 2022 tsakanin gwamnatin tarayya ta hanyar hukumar hana fasa kwauri ta kasa da kamfanin dake kula da shirin na TMP a matsayin wanda aka jinginarwa.
Shirin zai taimakawa hukumar kwastom da hanyoyi da dabaru na fasahar zamani wadanda zasu sanya hukumar ta zama hukuma dake gudanar da ayyukanta yadda yakamata da kula da harkokin kasuwanci da sauran hukumomin gwamnati.
Kari kan ci gaban fasahar zamani da samar da na’urori na fasaha, kamfanin dake kula da shirin zai taimakawa ayyukan hukumar hana fasa kwauri ta kasa ciki har da kula da na’urorin da horar da jami’anta daga ranar da aka fara aiwatar da shirin har zuwa shekaru 20 na jinginarwa da aka tsara.
Acewar bayanan da aka yiwa manema labarai kan aiwatar da shirin, za a aiwatar da shirin ne a matakai daban daban, inda mataki na farko ke kan hanya.
“Daga ranar 31 ga watan Disamba na 2023, shirin na TMP ya himmatu wajen samar da zuba hannun jarin dala miliyan 400 a matakin farko na shirin. Sama da jami’an kwaston 2, 500 za a bawa horo a farkon shekerar 2025 bisa tsarin horarwa na shirin.
“Horar zai hada da na tsare-tsare da tafikarwa da kula da na’urori da kuma sanin yadda shirin yake kaitsaye. Kamar yadda yarjejeniyar jinginawar ta tanada, kamfanin dake kula shirin na TMP ya samar tare da zana dukkan na’urori da manhaja na fasahar zamani da ake bukata.
“Hakan zai tabbatar da hukumar hana fasa kwauri ta kasa tana da cikakken sani da dukkan na’urori da fasahar da aka yi amfani da ita”, inji bayanan.
