Connect with us

News

Zamanantar da Ayyukan Hukumar Kwastom Babban Cigaba ne A Najeriya 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Najeriya har yanzu na ci gaba da fuskantar kalubalen koma baya, ta fuskar tattara kudaden haraji wadanda akan hada da sauran kudaden shiga da kasar ke samu wajen aiwatar da manyan ayyukan da yan Najeriya ke shaidawa.

Advertisement

Wannan kuwa na zuwa ne duk da yadda Najeriya ke da tarin albarkatun man fetur a sassan kasar, amma kuma har yanzu ana samun tsaiko wajen iya aiwatar da manyan ayyukan ci gaban da suka kamata ko kuma gwamnati ke aiwatarwa.

Eid-el-Kabir: Ya Kamata Mutane Su Guji Cin Naman Da Ya Wuce Kima Da Zafi Domin Yana Iya Cutar Da Lafiya —Dr Labaran 

Advertisement

Asusun bayar da lamuni na Najeriya IMF a watan Disambar 2023, ya ce Najeriya duk irin kokarin da mahukunta ke yi bai wadatar ba, domin kuwa har yanzu abun da kasar ke iya samu ta fuskar kudaden haraji kwalliya bata iya biyan kudin sabulu.

Kuma wannan koma bayan ana ganin ba zai haifar da da mai ido ba ga kokarin inganta rayuwar yan kasar, lamarin dake kara bayyana bukatar samar da sabbin dabaru wajen ingantawa tare da fadada bangaren tattara haraji ga gwamnatin tarayya.

Advertisement

 

Ya yin da yake jawabi a wajen gabatar da kasafin kudin kasar nan na wannan shekara, ministan kasafin kudi na kasa, Atiku Bagudu ya bayyana karbar haraji da sauran hanyoyin samun kudin shiga a matsayin hanyoyin da zasu taimaka wajen ganin kasafin ya samu kaiwa ga inda ake fata, a don haka yace yanzu haka ma’aikatarsa na aiki don bibiyar yadda ake tara harajin kasar nan, da sauran tsaruka wadanda ke a alaqa da tattara haraji a Najeriya.

Advertisement

 

 

Advertisement

A watan Oktoban 2023, mataimakin darakta a asusun bayar da lamunin IMF, mai kula da da sashin da suka shafi harkokin tattara haraji, ya yin da yake jawabi a wajen wani taro da Bankin duniya hadin gwiwa da IMF a Marrakesh dake Morocco ya ce bangaren tattara harajin Najeriya na ci gaba da fuskantar koma baya, idan aka kwatanta da kasashe maso tasowa.

 

Advertisement

A domin kawo karshen wannan kalubale tuni gwamnatin tarayya ta fara samar da wasu sabbin tsare tsare da zasu taimaka wajen kaucea kalubalen tare da samun damar iya rabauta tagomashin da akan samu a bangaren tattara haraji.

 

Advertisement

 

Daya daga cikin shirye shiryen sun hadar a Shirin zamanantar da ayyukan hukumar Kwastom, wanda tsohuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar a shekarar 2022, a kokarin gamnatin tarayya na rage yawan dogaro da bangaren man fetur dama abun da ake samu a bangaren.

Advertisement

 

Manufar samar da shirin ita ce domin yin duk mai yiwuwa wajen samar da sauyi ga ɓangare ko yadda ake tattara haraji a kasar nan, a kokarin gwamnati na ganin an rage yawan dogara aka man fetur d arzikin dake bangare.

Advertisement

 

Gundarin abun da ake fatan cimma karkashin shirin sune samar da sauyi mai ma’ana ga yadda hukumar Kwastom ke tattara haraji a kasar, bunkasa bangaren kasuwancin kasar ta hanyar samar da yanayi mai kyau musamman ga masu zuba jari, da kuma dakile ayyukan cin hanci a bangaren Tattara kudaden shigar.

Advertisement

 

 

Advertisement

Ana Aiwatar da shirin ne karkashin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kan su wanda ake kira PPP, Inda aka cimma yarjejeniyar jinginarwa a ranar 30 ga watan Mayu na shekarar 2022, tsakanin gwamnatin tarayya ta hanyar hukumar Kwastom da kamfanin dake kula da shirin TMP a matsayin wanda aka jinginarwa.

 

Advertisement

Kari kan ci gaban fasahar zamani da samar da na’urori na fasaha, kamfanin dake kula da shirin zai taimakawa ayyukan hukumar hana fasa kwauri ta kasa ciki har da kula da na’urorin da horar da jami’anta daga ranar da aka fara aiwatar da shirin har zuwa shekaru 20 na jinginarwa da aka tsara.

 

Advertisement

Daga ranar 31 ga watan Disamba na 2023, shirin na TMP ya himmatu wajen samar da zuba hannun jarin dala miliyan 400 a matakin farko na shirin. Sama da jami’an kwaston 2, 500 za a bawa horo a farkon shekerar 2025 bisa tsarin horarwa na shirin.

 

Advertisement

Horon zai hada da na tsare-tsare da tafikarwa da kula da na’urori da kuma sanin yadda shirin yake kai tsaye. Kamar yadda yarjejeniyar jinginawar ta tanada, kamfanin dake kula shirin na TMP ya samar tare da zana dukkan na’urori da manhaja na fasahar zamani da ake bukata.

 

Advertisement

 

Shirin dai ana yinsa a matakin rukuni rukuni, bisa tsari mai kyau kuma da inganci wanda ya kunshi, mataki har zuwa 3, da ake fatan aiwatarwa a tsawon shekaru 20, Shekaru daga 1 zuwa 6 samar da na’uara ciki har da na’urar zahiri da na fasahar zamami, yayin da Daga shekara 7 zuwa 13 Kula da tsarin shirin da maye gurbin na’urori da ake bukata, sai kuma Shekaru 14 zuwa 20 da ake fatan a mayar da tsarin zuwa ga jami’an hukumar kwastom tare da tallafin shirin na TMP wajen basu horo.

Advertisement

 

Tsarin amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan hukumar Kwastom, yana samun kulawa ne tun bayan taro kan bunkasa kasuwanci da majalisar dinkin duniya ta gudanar, wanda kuma yanzu haka kasashen sama da 80 ne a fadin duniya ke gudanar da wannan da shiri, kuma kungiyar tarayyar Turai ta kaddamar da fara wannan tsarin na tafiya da zamani ga kasashen dake karkashin ta tun a shekarar 1990, kuma ya taka rawa matuka wajen bayar da yanayi mai ga don kasuwancin da ake son yi.

Advertisement

 

A bangaren kasar Amurka kuwa, ta samar da wani dandali ne ga yan kasuwa da ta basu damar suyi amfani da shi, wajen samun damar a tantance musu kayan da suke fatan shigar da su kasar ko fitar da su, duk ta hanyar amfani da Intanet.

Advertisement

 

Makamancin wannan mataki ne hadaddiyar daular Larabawa ta dauka, ita kasar China haka, wato dai sun zamanantar da yadda suke kasuwancin da abokan huldarsu a baya, kuma yayin da Dubai da China suka koma kan tsarin kamfanin Huawie ne ya zama babban abokan huldarsu akasuwancin, kuma abun yabawa shima kamfanin yanzu haka yana daga cikin kusoshi a gudanar da sabon shirin a Najeriya.

Advertisement

 

Mahmud is the Deputy Editor of PRNigeria and wrote via: babasalam1989@gmail.com.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending