Connect with us

News

Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano.

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

A yayin da aka samu raguwar ayyukan fadan Daba da kuma kwacen Wayoyin mutane a fadin jihar Kano sakamakon sabbin dabarun da Jami’an Tsaro suka bullo da shi .

Sai dai kuma yanzu lamarin fadan Daba yazama wata babbar Barazana ga Unguwanne da dama kamar Unguwar Ja’en dake Sharada da kuma wasu Unguwanne dake karamar Hukumar dala dake Jihar Kano.

Fadan daba ya haifar da zaman dardar a unguwannin Goran dutse da kuka Bulukiya da wani yanki a Dala

Haka Zalika an sarewa wani matashi hannu a unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, biyo bayan faɗan faɗan Dabar da ya faru yankin, har aka kashe kwamandan Bijilanten yankin a daren ranar Talata.

A zantawar Gidan Radiyo Dala FM Kano, da matashin ɗan unguwar Mundaɗu da ke Kano, ya ce, ya shiga unguwar ya Ja’en ƴan Dillalai ne daga unguwar su domin zuwa gaishe da kakannin sa, inda bai yi aune ba ya rinƙa jin sara daga wasu ƴan Daba a yankin, lamarin da suka sare masa hannu.

Rahotanni na nuni da cewa bayan Sallah da Kwana biyu akayiwa wani mutum da baijiba baiganiba yankan Rago a bayan Makabartar Kuka bulukiya.

Advertisement

A baya dai rundunar Yan Sanda ta bude kofar karbar tuba da gyara daga ’yan daba a Kano, wanda hakan ya kai ga ajiye makaman kusan ’yan daba 50 a jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce Rundunar yan sanda ta samu nasarar cafke mutum daya daga cikin ƴan dabar da ake zargin sun kashe kwamandan ƙungiyar Bijilante na unguwar Ja’en dake jihar Kano, mai suna Muhktar Garba, wanda akafi sani da Baballiya.

Kiyawa ya ce bayan samun rahoton faruwar faɗan dabar a tsakanin ƴan unguwar Ja’en Maƙera, da kuma wasu ƴan unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, ne aka tura jami’an ƴan sanda don su samar da tsaro a yankin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending