News
Hukumar NDLEA Ta Kama Matasa Maza Da Mata 60 Da Suke Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, a ranar Lahadi, ta kai samame wani gida da matasa suke dabdalewar shaye-shayen kwayoyi da ganye inda ta kama mutane 60.
Kakakin hukumar Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kaiwa matasan samame bayan sun samu bayanan sirri game da wannan dabdalewa da suka shirya yi.
Abinda ya sa na ki karbar cin hancin naira miliyan 150 daga wani dan kasuwa – Jami’an Dan Sanda
An kama mata 35 da wasu maza 25 maske sun rankwale da kwayoyi, suna bushe-bushe naɗaɗɗun mandula na wiwi da wasu kwayoyi.
Wasunsu an sake su bayan sun biya tara wasu kuma suna tsare hannun ƴan sanda.
Matasan dai suna bukin nuna wanda ya iya dakewa ne bayan ya yi matuƙar maskewa, ya haɗiyi kwayoyi batare da ya nuna gazawa ba.
An kama su a wani gida dake rukunin gidaje na Sun City dake Abuja.
A cikin matasan da aka kama an samu wasu mutum shida da ke ɗauke da wasu sunadarai na musamman na rankwalewa, waɗanda aka kama sun haɗa da Victoria Adoga, Hamza Yari, Joanne Essein, Socchima Valentine Jago Imole da Charles Indobuibisi.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
