Connect with us

News

Za A Shafe Kwanaki Uku Ana Zabga Mamakon Ruwan Sama  Da Tsawa Daga Lahadi – Hukumar NiMet 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen tsawa da mamakon ruwan sama daga ranar Lahadi zuwa Talata a fadin kasar.

Advertisement

An fitar da hasashen yanayi na NiMet ne ranar Asabar a Abuja, inda aka yi hasashen za a yi tsawa a ranar Lahadi da ruwan sama a wasu sassan jihohin Adamawa, Taraba, Borno, Kebbi, Kaduna, Gombe, da Yobe da safe.

Sabon Mafi Karancin Albashi Buhun Shinkafa Kadai Za A Iya Saye Da Shi  —Ndume 

A washegari, ana sa ran za a yi tsawa a duk fadin yankin Arewa. Ana sa ran ruwan sama a yankin Arewa ta tsakiya da safe.

Advertisement

An yi hasashen tsawa mai matsakaicin karfi tare da ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Filato, Benuwe da Kogi.

Inda kuma ake sa ran samun ruwan sama na tsaka-tsaki da safe a sassan Ondo, Ogun, Edo, Bayelsa, Cross River, Rivers, Akwa Ibom da Delta.

Advertisement

Saboda haka, NiMet ta shawarci mazauna yankunan da su guji wuraren da ambaliyar ruwa ta fi kamari domin akwai yiwuwar ambaliya a manyan biranen kasar sakamakon mamakon ruwan sama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending