News
Rikicin Masarauta: Yadda Wasu Mutane Sukaiwa Dan Majalisar Dokoki Duka A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu gungun mutane sun yiwa Dan Majalisar Dokokin Jihar Kano Abdul-Majid Umar Wanda akafisani da Mai rigar fata dukan tsiya a wani taron da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero ya halarta a ranar Asabar.
Mai rigar fata Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwale, wasu ‘yan mazabarsa ne suka kai masa harin a Unguwar Goron Dutse.
Dan majalisar a ranar Litinin din da ta gabata ya ce tsohon sarkin da ‘yan sanda sun kubutar da shi daga hannun mutanen.
Aminu Ado Bayero, a ranar Asabar din da ta gabata, ya halarci taron rufe taron shekara-shekara na zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano, wanda shugabannin darikar Tijjaniyya suka shirya a gidan Isyaku Rabiu da ke Goron Dutse, a karamar hukumar Gwale ta jihar.
Umar ya zauna a gefen sarki a wajen taron amma an kai masa hari jim kadan ne bayan barinsa wurin taron.
Kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito, mutanen sun zarge shi da goyon bayan kudirin tsige sarkin.
Rahotanni sun ce al’ummar sun raunata dan majalisar kafin ya tsere zuwa cikin motar ‘yan sanda da ke sintiri.
Dan majalisar ya shaidawa sashen Hausa na BBC a ranar Litinin cewa, dubban magoya bayan hambararren sarkin ne suka kai masa hari bayan ya bar taron ba tare da sanin ya kamata ba.
Umar ya ce ya bar wurin ne a lokacin da ya lura babu tsaro, ya yanke shawarar barin ne lokacin da ya lura shi kadai ne jami’in gwamnati a wajen taron.
“Na kara shiga damuwa bayan na bar wurin taron yayin da mutane dauke da muggan makamai suka far min. Na yi sauri na shiga motar ‘yan sanda. Haka aka kubutar da ni daga wannnan harin.
“Magoya bayana biyu sun jikkata yayin da muke barin wurin taron”, in ji dan majalisar.
Sai dai daya daga cikin hadiman sarkin da aka tube, Khalid Adamu a kafafen yada labarai ya musanta cewa maharan suna cikin tawagar su.
Ya ce, Aminu Ado ya isa wurin taron ne da dimbin magoya bayansa, amma babu daya daga cikinsu da ke dauke da makami.
Rikicin masarautar Kano ya fara ne bayan da ‘yan majalisar a ranar 23 ga Mayu, 2024 suka soke dokar majalisar masarautun jihar ta 2019, wanda a karkashinta tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu hudu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
