Connect with us

News

Dan Mu Ba Tela Bane Hasali Ma Bai Taba Hawa Keken Dinki Ba —Iyalan Matashin Da DSS Ta Kama

Published

on

FB IMG 1723387617120

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Yan uwan Matashin Da Jami’an Tsaro suka kama Suke zarginsa da Dinka tutar Ƙasar Russia sun bayyana Cewa Matashin ba tela bane Kuma Bai taba yin dinki ba.

Yan uwan Matashin sun bayyana Damuwarsu akan Yadda Jami’an Tsaro suka kama Matashin Tare da Zargin Cewa Shine Yake Dinka tutar

Kotu Ta Tura Jagororin Zanga-Zanga Gidan Gyaran Hali A Katsina

Suna Mai Cewa Matashin Mai Suna Ahmad Yusuf Muhammad, Bai Shiga Zanga Zangar da akayi ba, Sakamakon Gargadi da Iyayensa Sukayi Masa

Amma acewar Yan uwan nasa Sunyi Mamakin Yadda Jami’an Tsaro suka Ce, wai Shine Yake Dinka tutar Ƙasar ta Russia

Ta Yaya Wanda Bai Taba dinki ba, Kuma Bashi da Keke Kuma ace an kama shi Amatsayin Wanda Yake Dinka tutar? acewar Yan uwan Matashin

Advertisement

Sun Bukaci Jami’an Tsaro Suka bincike akan Wadanda Ake Zargin Tare da Kira da Saki Dan uwan nasu, Tunda acewar su Bashi da alaka da Abinda ake Zargin sa Dashi.

Daily Trust ta  rawaito abaya bayan nan ne Jami’an Tsaro suka Kama Mutane da yawa da Laifin Daga Tutar Ƙasar Russia, ciki harda Matashin da Yan uwansa Suka Ce, Bashi da Hannun

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending