News
Manya-Manyan ‘Yan Adawa A Najeriya Na Tattaunawa Kan Hadaka Gabanin Zaben Shekarar 2027
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Manya-manyan ‘yan adawa uku Atiku Abubakar na Jamiyyar PDP, Peter Obi na Jamiyyar Labour Party da Rabiu Kwankwaso na Jamiyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a Najeriya na tattaunawa kan yiwuwar hadaka gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Manya-Manyan ‘Yan Adawa A Najeriya Na Tattaunawa Kan Hadaka Gabanin Zaben Shekarar 2027
Abdullahi ya ce, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don ceto Najeriya a cikin kangin da jam’iyyar APC ta cefa kasar a shekarar 2027.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
