News
Gwamnatin Tarayya Ba Ta Umarci Kamfanin NNPC ya Ƙara Farashin Litar Man Fetur Ba
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata rahotanni da ke ta yawo a shafukan jaridu da na sada zumunta cewa wai ta umarci kamfanin mai ƙasa ya kara farashin litar man fetur a Najeriya.
Minista Heineken Lokpobiri ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar ranar Talata.
Mazauna garin Abuja sun wayi gari ranar Talata da layukan mai a cikin babban birnin Najeriya, tare da kara farashin zuwa har naira 1000 a wasu gidajen man.
” Ƙaryata wannan batu ya zama dole daga gwamnati. Domin karya ake ya , gwamnati bata umarci NNPC ya kara farashin litar man Fetur ba.
Kamfanin NNPC na zaman kansa ne, babu dalilin da ya sa gwamnati zai saka masa baki wajen harkar sa. Amma a riƙa kage ana cewa wai gwamnati ta umarce kamfanin NNPC ta ƙara farashin man Fetur ba gaskiya ba ne.
