Connect with us

News

Farashin man fetur ya tashi a kasuwar duniya

Published

on

Farashin man fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan da manyan ƙasashe masu arzikin man fetur suka bayyana rage adadin man da suke fitarwa.

Farashin ya ƙaru da fiye da kashi biyar cikin ɗari, inda ya kai sama da dala 84 a kan kowacce ganga.

Advertisement

An Tisa Keyar Mabarata 217 Daga Abuja Zuwa Jihohinsu Na Asali

Ƙaruwar farashin na zuwa ne bayan ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC suka ayyana cewa za su rage yawan man da suke fitarwa zuwa kasuwar da fiye da ganga miliyan ɗaya a kowacce rana.

Ko a watan Fabrairun bara ma, sai da farashin man ya tashi, bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Advertisement

To sai dai sannu-a-hankali farashin ya ci gaba da sauka, inda har ya koma yadda yake kafin mamayar.

Masu sharhi na cewa ƙaruwar farashin zai kawo cikas, a ƙoƙorin da duniya ke yi wajen rage hauhawar farashin kayayyaki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending