Connect with us

News

Za’a Kara Kudin Alawus Na Yan Bautar Ƙasa – Hukumar NYSC

Published

on

NYSC Members 700x430

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar NYSC ta tabbatarwa da ƴan yiwa ƙasa hidima cewa za a ƙara kuɗin alawus na N33,000 da ake biyan su a duk wata da zarar gwamnatin tarayya ta aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙarancin.

Advertisement

Shugaban hukumar NYSC, Yusha’u Ahmed, shine ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ya ziyarci jihohin Kebbi da Sokoto domin jawabi ga ƴan yiwa ƙasa hidima na 2024 Batch ‘B’ na biyu a sansanonin horaswa na jihohin biyu.

Daurarru Na Mutuwa Saboda Yunwa A Gidajen Yarin Najeriya 

Ya bayyana cewa gudunmawar da ƴan yiwa ƙasa hidima ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa yana da matuƙar muhimmanci, inda ya jaddada cewa ya kamata ƴan yiwa kasa hidima su yi amfani da shekarar hidimar su wajen bunƙasa kansu da shirya wa kansu ingantacciyar makoma.

Advertisement

Ya kuma ƙarfafe su da su yi amfani da damar da shirin NYSC na koyon sana’o’i da bunƙasa kasuwanci ya bayar.

Shugaban hukumar ya ce, “Aƙalla, ku koyi sana’a yayin da kuke sansanin, kuma bayan kammala tsarin horaswa, dama bayan fita daga sansanin.

Advertisement

Ku yi ƙoƙarin koyon sana’ar da za ta ba ku damar ƙirƙirar ayyukan yi da ɗaukar ma’aikata maimakon neman aikin yi. Muna da tsofaffin ƴan yiwa ƙasa hidima da yawa a faɗin ƙasar da suke yin nasara a cikin sana’o’in su daban-daban a yau.”

“Hukumar NYSC ta haɗa hannu da ƙungiyoyi masu nagarta da yawa kamar Babban Bankin Najeriya (CBN), Bankin Masana’antu (BOI), Unity Bank, Access Bank, da gidauniyar NNPC da sauransu, waɗanda ke taimakawa wajen ba da rance da tallafi ga ƴan yiwa ƙasa hidima.”

Advertisement

Ya tabbatar musu da cewa za a tabbatar da tsaron lafiyar su a duk tsawon shekarar hidimar su.

Ya ce za a tura ƴan yiwa ƙasa hidima zuwa wuraren da ke da tsaro amma ya shawarce su da su kasance cikin shiri da lura da yanayin da ke kewaye da su.

Advertisement

A jawabin ta, ko’odinetan NYSC na Jihar Kebbi, Aghata Banki-Okolo, ta bayyana cewa ƴan yiwa ƙasa hidima sun saba da rayuwar sansanin sosai.

“Sun amsa da kyau ga dukkan ayyukan sansani da umarnin da ake ba su. Har ila yau, muna da jimillar jami’ai da suke aiki a sansanin 240 waɗanda ke amfani da basirar motsin zuciya wajen gudanar da ayyukan su.”

Advertisement

“Jimillar ƴan yiwa ƙasa hidima 1,195 ne aka yi wa rajista, wanda ya ƙunshi 1,077 na Jihar Kebbi da kuma 118 waɗanda aka kwaso daga Jihar Zamfara,” in ji ta.

A nasa ɓangaren, ko’odinetan NYSC na Sokoto, Yakubu Usman, ya kuma yaba da ɗabi’un ƴan yiwa ƙasa hidima da saurin da suka yi wajen sabawa da yanayin sansanin.

Advertisement

Usman ya bayyana cewa jimillar ƴan yiwa ƙasa hidima a Jihar Sokoto sun kai 1,488, ciki har da maza 682 da mata 806, wanda ya haɗa da maza 134 da mata 66 waɗanda aka kwaso daga Zamfara sakamakon barazanar tsaro.

A watan Yuli, ƙungiyoyin ƙwadago sun amince da mafi ƙarancin albashi na N70,000 bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya.

Advertisement

Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da dokar ƙara mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 a ranar 23 ga Yuli, kuma aka sanya hannu kan dokar a ranar 29 ga Yuli.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending