News
Matasa Sun Cafke Wani Matashin Da Ya Sassare Mahaifinsa Da Adda Ya Kuma Yanke Gaban Dansa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Matasa a kauyen Umudosi dake karamar hukumar Obingwa jihar Abia, sun cafke wani matashi mai suna Amadi Alozie da ya sassare mahaifinsa da adda.
Matasan na zargin cewa Alozie dan kungiyar asiri ne saboda ya yanke gaban dansa dan karamin yaro.
Amfani Da Sabulun Dove Na Hana Haihuwa Tare Da Da Lalata Fata – Hukumar NAFDAC
Alozie ya kama dansa domin ya yanke masa gaba inda a dalilin ihun da yaron yi mahaifiyar matashin Mrs Alozie ta rugo da gudu domin ganin dalilin ihun yaron.
Ganin mugun abin da danta ke kokarin yi ne Alozie ya zaro sharbebiyar adda ya sare mahaifiyarsa nan take da fadi ta mutu.
Alozie ya yi kokarin arcewa bayan da ya aikata wannan ta’asa amma sai matasan kauyen suka kama shi suka hada shi da ‘yan sanda.
Dan karamin yaron da Alozie ya yi kokarin yanke wa gabansa na asibiti likitoci na duba shi a dalilin raunin da mahaifinsa ya ji masa.
Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Maureen Chinaka ta ce Alozie na tsare a ofishin su suna gudanar da bincike a kansa.
