News
Kotu Ta Umarci A Tsare Magidanci Har Sai Ya Kammala Tunanin Yadda Zai Kula Da Iyalinsa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata Kotu Shari’a a Kaduna, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare wani Musa Hussaini na tsawon awanni domin ya yi tunani akan yadda zai samu kudin kula da ‘ya’yansa guda hudu.
A baya, tsohuwar matarsa, uwa ga yara hudu, Hajara Sani, ta roki kotu da ta taimaka mata wajen dawo mata da wasu kayanta daga hannun Hussaini.
An Ci Tarar Kamfanin Lantarki Naira bilyan 1.6 Saboda Tsugaga Wa Kwastomomi Kudin Bil
Ta shaida wa kotu cewa Hussaini ya sayar da kujerunta guda biyu da talabijin ɗinta, sannan ya tilasta mata sayar da gadonta.
”Na ba shi kudin da na sayar da gadona jim kaɗan kafin ya sake ni.
“Ina so kotu ta tabbatar da saki uku da Hussaini ya yi min, sannan kuma ta umarce shi da ya dauki nauyin kula da yarana guda hudu,” in ji ta.
A martaninsa, Hussaini ya tabbatar da yin sakin uku a lokuta daban-daban, inda ya kara da cewa ya sayar da kayan da amincewar mai kara domin gyara kayan aikin sa na tukin mota.
Ya ce ya sayar da talabijin da kujeru akan Naira 5,000 sannan ya karɓi Naira 6,500 daga mai kara bayan gadon an sayar da shi.
WIKKI TIMES ta ruwaito cewa ya roki kotu da ta ba shi damar biyan kudin da kadan kadan, yana mai cewa, “Zan rika ba ta Naira 2,000 a kowane mako.”
Da aka tambaye shi game da walwalar yaransa, ya ce, ba shi da wani tanadi ko shiri na kulawa da su a halin yanzu.
Alkalin kotun, Malam Mukhtar Aliyu, ya bayar da umarnin tsare wanda ake tuhuma na tsawon awanni domin ya yi tunani akan yadda zai kula da yaransa, sannan ya dage shari’ar zuwa 25 ga Satumba don ci gaba da sauraron kara.
