News
Yan Sandan Sun Kama Wani Basarake Da Ake Zargi Da Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Katsina
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kama wani Basarake a Jihar Katsina da ake zargi da hada baki da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suna karbar diyya.
Mai magana da yawun rundunar Abubakar Sadiq Aliyu ya ce jami’an tsaro sun kama Usamata Adamu, mai unguwar Tambai a karamar hukumar Safana da laifin gabatar da bayanai ga ‘yan bindigar da suka addabi yankin.
Kakakin ‘yan sandan yace bayanan asiri da suka samu ya sa suka bi sawun Basaraken zuwa Sabon Gida dake karamar hukumar Igabi a jihar kaduna inda suka kama shi.
Aliyu ya ce tuni Basaraken ya amsa laifinsa tare da gabatar da sunayen wasu mutane 2 a kauyen Runka dake taimaka masa. Gwamnan Katsina Dikko Radda ya dade yana zargin wasu mutanen dake hada baki da ‘yan bindiga domin satar jama’a da kuma garkuwa da su a jihar.
Daily Trust
